A yau Lahadi ce 2 ga watan Fabraiyu na wannan shekara, wanda yayi dai-dai da 3 ga watan Shaban ranar haihuwar tauraro na 3 daga cikin limamai masu tsarki daga cikin iyalan gidan manzon All..(s), har’ila yau shi ne ranar “tsaro” nan JMI.
Imam Hussain (a) shine limami daga cikin liamai masu tsarki wadanda suka bada jininsu, da shi da jama’a kadan da suke tare da shi suka sayar da rayukan su don ganin addinin manzon All..(s) ya tabbata a bayan kasa.
Imam Khumaini (q) wanda ya kafa JM a nan Iran ya sanyawa wannan ranar nanar (tsaro) a kasar Iran don mutanen kasar su dauki darasi daga rayuwarsu su kuma yi amfani da abubuwan da suka faru a Karbala da shi Imam Husain (a) don kare JMI daga makiyanta. Su bada ransa kamar yadda Imam Hussain (a) ya bada randa don kare asalin addinin musulunci, addinin gaskiya.