Al-Adu Da Ci Gaban Addinin Musulunci A Tarihi 22

22-Asslamau alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na al-adu da ci gaban addinin musulunci a tarihi, wanda ni

22-Asslamau alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na al-adu da ci gaban addinin musulunci a tarihi, wanda ni Tahir Amin nake kawo mako sau guda a ko wane mako. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.

///…Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun yi maganar ayyukan masana ilmin taurari na musulmi da kuma yanda suka kawo ci gaba mai yawa a wannan fannin, kuma turawan kasashen yamma sun yi amfani da ci gaban da wadannan masana suka kawo amma basu ambacesu a cikin littafansu ba.

Mun yi maganar yanzu masana musulmi suka gani yanda ake gwajin lokaci da bambancinsa tsakanin garuruwa tun zamanin sarki Mamun daya daga cikin sarakunan Abbasiya, ko kuma kayakin aikin gwajion lokaci, da kayakin aikin gano girma da tsawo tssunuka da koguna. Sannan mun ambaci yanda masana musulmi suka gano duniyarmu ce take zagaya rana ba akasin haka ba kamar yanda masana kasar girka ptolemy ya tafi a kai kafin musulmi. Amma masana musulmi suka gano kuskurensa sannnan suka gyara . amma a lokacinda masana turawa suka zo bayyana wannan ilmin shekara dari 9 bayan haka sai suka nasabta hakan ga kansu.

A cikin shiye shiryemmu da suka gabata mun ambaci masana musulmi da kuma rawar da suka taka wajen kawo ci gaba a ilmin lissafi da taurari, da kuma muhimman ci gaban da suka samar a wannan fagen.

Da yardar All.. a cikin shirimmu na yau zamu fara magana kan ilmin kanikanci da physics da kuma gudumawar musulmi a wajen bunkasa su. Kamar yanda binciken da muka yi dangane da gudumawar masanamusulmi a ilmin lissafi da taurari a cikin tarihi, kuma yake da kayatarwa. Hakama gudumawarsu ailmin kanikanci da kimiyyar lissafi ko Physics da zamu fara yake da muhimmanci ga jan hankali.

Masana musulmi sun samarda sabbin ilmi da ci gaba mai yawa, a fegen ilmin kimiyyar lissafi a tarihin musulunci. Sai dai har yanzun an gafala daga sanin muhimmancin irin ci gaban da suka samar a fagen ilmin kimiyyar lissafi da kanikanci kamar yadda yake a wadanda muaka yi maganarsu.

Sannan masana da malaman tarihi, su ma suna gafala sau da dama wajen ambatun wadan nan al-amura. Don haka a cikin shirimmu na yau zamu fara magana dangane da irin ci gaban da masana da malaman ilmin kanikansu musulmi suka samar a tarihi. Ku kasance tare da mu.

Ilmin kanikanci a wajen musulmi shi ne suke kira ilmin ‘Al-Hiyal, ko ilmin dabarbaru ko kuma Dabarbaru.

Wannan ilmin, tare da kayakin aiki na musamman wadanda suke kebe shi, yana da matukar muhimmanci kuma shi ne ake kira kanikanci a wannan zamanin.  

A tsarin aji ajin da suka yiwa ilmomi, malamai masana musulmi sun sanya ilmin kanikanci cikin dabaka da ilmomi kamar Lissafi, taurari, wake, inginiya da sauransu. Yake yake da kiristoci, da tarjama da kuma musayar ilmi suna daga cikin hanyoyin da ilmin kanikanci ya shigo kasashen musulmi sannan daga baya ya koma wajen kasashen yamma.

Sai dai a fannin kanikanci, littafai kanan ne aka tarjama daga harshen larabci zuwa turanci ko kasashen yamma.

A yake yaken salibiyya ko kiristoci da musulmi, a lokacin, sun yi mamakin irin ci gaban da musulmi suka sami a kayakin yaki. Sun kera agoguna daban daban masu lissafin lokuta da dikka. Babu kuskure. Kuma suna amfani da ruwa ko kuma nau’ii daban daban na makamashi.

Suna da kayakin aiki daban daban na naukar abubuwa masu nauyi. Kamar (Krent).

Abanda haka suna da kayakin yaki daban daban , wadanda kiristoci daga kasashen yamma a lokacin basu da su. Wadanda suke nuna irin ci gaban da musulmu suke da shi a lokacin.

Atakaice, muna iya cewa, a yanke ci gaban musulmi a ilmin kanikanci ya fito ne, ko ya samo asali ne daga yankin gabas ta tsakiya, musamman daga kasashe kusa da tekun medeteranina. Mun san cewa, mutanen kasar Masar da kuma Romawa suna da ilmin kanikanci tun da dadewa. Sai dai rabon mutanen girka ya fi yawa.

A  zamanin sarakunan Abbasiyawa, an tarjama littafai da dama zuwa harshen larabci  daga yaren Girka, ko siryananci. A wancan lokacin, an ce musulmi sun sami wata takarda karama mai matukar muhimmanci dangane da kera agogo wanda kuma ake dangantawa da Archimedes. Jazari yace wannan takardan ita ce masomin ulmin kanikanci a wajensa.

An  san cewa Badi’uz Zaman shi ne mafi shahara a ilmin kanikanci a lokacin.

Ya rayu a rabi na biyu a karni na 6 zuwa farkon karni na 7 a yankin Diyar Bakr . An ce Hakimin Diyar Bakr na lokacin ne, mai sun Sarki Saleh ya bukaci Jarzi ya rubuta littafinsa dangane da kanikanci.

Ayyulan Jazri a fannin kanikanci, kama daga rubuce rubucensa da kuma kere kerensa, sun zama makoma ga masana da dama a kan ilmin kaninkanci, harma suna masa lakabi  da shugaban injiniyoyi.

Ya shahara saboda ilmin kanikanci da yake da ci, da kuma ayyukansa a fili na kere kare. Shi mutum ne mai kirkire kirkire, kuma ayyukansa suna da anganci da kuma kyau.

Ya iya bayanin yanda za’a yi amfani da kayakin aiki daban daban a ayyukan kanikanci, kuma yana himmatuwa wajen jarrabawa saninsa a aikace, har zuwa lokacin da zai kore a aikin. Ya kasance baya amincewa da duk ilmin da ba’a jarraba shi aka gani ba.

Kirkire kirkire da sabbin kare karen da Jazri ya yi a ci gaban musulmi suna dai dai da ci gaban da indiyawa da Iraniyawa da irakawa suka samar ne.

Kari kan kwarewar Jazri kan fannonin ilmin kanikanci na musulmi, ya samar da wasu adadi masu yawa na kayakin aikin handasa, da na’urori aikin kanikanci, kamar inda ya kera ko ya gina ingina na Haidrolic da na tururi da injina masu amfani da makamashi. Wanda ko a wannan zamanin mutum yana iya gano ko kuma sanin irin ayyukan kanikancin da wannan masanin yake da shi.

Daya daga cikin littafansa dangane da ilmin kanikanci sun hada da

 (( اَلجامعُ بین العلم و العمل ، النّافعُ فی صناعة الحِیَل.

Wato “mahadar ilmi da aiki, mai amfani a cikin masana’antar kerekere,) ko nau’in hydrolics, (masu amfani da makamashi) ko kanikanci. Wannan shi ne rubutu mafi amfani  wajen sanin kayakin aikin kanikanci a cikin shekaru daruruwan da suka gabata.

DUk wanda ya karanta wannan littafin zai ga bincike na ilmi, sannan tsarin aiwatar da fahintar a aikace kuma daki daki.

A cikin farkon karni na 20, masana ilmin lissafi kamar Wiedmann da Hauser yan kasar Jamus, sun gano muhimmancin wannan littafin, sun kuma kawo shi a cikin rubuce rubucensu na tarihin ilmi. Harma sun kawo wani bangare na wannan littafin a rubuce rubucensu. Sannan daga baya wani bature da ake kira Donald Hill ya tarjama wannan littafin sannan aka buga shi aka yada. Sai kuma a shekara 1979 wani masani musulmi mai suna Ahmad Yusuf Hassan ya dauki dawainiyar buga littafin Na jazri, wanda a halin yanzu yana cikin dakin ajiyar littafai na Shiek Shahid Murtadah Mutahhari dake nan Tehran.

Littafin Jazri, yana da matukan muhimmanci a fannin kanikanci, idan mutum ya karanta shi, don haka ne aka yi masa sharhuna da dama.

George Sarton, masanin tarihi ilmin tarihin ilmi, ya fada dangane da wannan littafi na Jazra, yana cewa, (wannan littafin shi ne mafi cikar littafin a wannan fannin nasa, kuma yana iya zama littafin mafi inganci a wannan fannin wanda musulmi suka rubuta.

Jazri ya littafin ( الجامع بین العلم و العمل ، النافع فی صناعة الحیل ) ya kawo nau’o’in kayakin aiki kinikanci, daga cikin har da agogon ruwa, agogon kitse, kayakin aikin daukar jini.  Injinan cilla ruwa sama, a lambuna, da sauran kayakin daga ruwa sama da sauransu.  Ya kuma bayyana hanyoyin kere dukkan kayakin kanikanci da ya samar.

Kuma har yanzun , masana’ant suna iya dogaru da bayanan da ya bayar a cikin wannan littafin su samar da kayakin aiki da dama wadanda zasu iya samarwa a cikin masana’antunsu.

Har’ila yau masana suna cewa har yanzun masana harkokin kanikanci sun ce akwai daya daga cikin injinan da Jazri ya gina har yanzun ana amfani da shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted