Arangama Ta Mamaye Zanga zangar Tsadar Rayuwa A Faransa   

Kungiyar kwadago ta CGT ta kiyasta mutum 500,000 da suka shiga zanga zangar a fadin kasar ranar Asabar 17 ga watan Oktoba 2026.

Rahotanni daga Faransa na cewa an yi arangama tsakanin jami’an tsaro da masu zanga zangar tsadar rayuwa a sassa daban daban na faransa da suka hada da Lyon, Marseille da kuma Paris babban birnin kasar.

Kungiyoyi da dama ne a faransa suka shiga jerin zanga zangar da daliban sakandare suka faro a kasar kan tarin matsalolin da suka ce suke fuskanta.

Daliban makarantun sakandare da na jami’a da kuma tsoffin ‘yan zanga-zangar da ake wa lakabi da Yellow Vest, da masu fafutukar kare muhalli, har ma da manoma da kungiyoyn kwadago sun shiga zanga zangar ta yau Asabar kan tsadar rayuwa da hauhawan farashin makamashi.

Zanga zangar dai na zuwa ne daidai lokacin da faransa ke tunkarar manyan zabukan a shekara mai zuwa, Wanda ya dawo da batun rawar da matasa ke takawa a siyasa kasar.

An bara ‘yan sanda da dama a biraren Paris da Marseille inda aka samu rahotanni arangama tsakanin bangarorin biyu inda ‘yan sanda sukayi amfani da hayaki mai sa hawaye a yankuna da dama.

Kafin tsakar rana, hukumomi sun kiyasta mutum 32,800 da suka shiga zanga zanga a sassan kasar, yayin da kungiyar kwadago ta CGT ta kiyasta mutum 500,000 da suka shiga zanga zangar a fadin kasar.

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta faransa ta ce an kama mutane 272 zuwa karfe 3 na yamma.

A Marseille, masu bore sun kai hari kan ofishin ‘yan sanda.

A Lyon, an yi wa ofishin yawon bude ido na birnin fashi aka kuma kone shi.

Kamfanin Dilancin Labaren AFP ya rawaito barkewar aranganma tsakanin jami’an tsaro da masu zanga zanga a Bordeaux.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted