A Karon Farko Yemen Ta Kakkabo Jirgin Yaki ‘Typhoon’

A karon farko dakarun kare sararin samaniya na kasar Yeman sun kakkabo jirgin yaki samfuran Eurofighter Typhoon, mallakin gwamnatin kasar saudia. Tashar talabijan ta Presstv

A karon farko dakarun kare sararin samaniya na kasar Yeman sun kakkabo jirgin yaki samfuran Eurofighter Typhoon, mallakin gwamnatin kasar saudia.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin sojojin kasar Yemen Burgedia Janar Yahyah Saree yana fadar cewa a ranar 15 ga watan Octoba dakarun kare sararin samaniyar kasar Yemen a Lardin sa’ada sun sami nasarar kakkabo jirgin yakin Eurofighter Typhoon kirar kasar Burtania, wanda kuma ya fara aiki kimani shekaru 20 da suka gabata a duniya.

Jirgin wanda ake kirari da wanda ba za’a iya kakkaboshi ba, ya fada cikin tarkon sojojin kasar Yemen ya kuma fada kasa. Jirgin Eurofighter Typhoon, yana gudu fiye da saurin sauti. Gwamnatin sarakunan Saudia sun sayi jiragen gudu 72 kan fam din ingila biliyon &4.4  daga kamfanin British BAE Systems na kasar Burtania a shekara ta 2007.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted