Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya isa birnin Bagdaza na kasar Iraki a safiyar yau Asabar 17 ga watan Octoba, don halattar taron kungiyar kasashen musulmi ta OIC, amma kafin ya shiga gari ya yada zanga a wurin da Amurka ta kashe Janar Qasim Sulaimani da Mahdi Al-Muhandis don girmama su.
Tashar talabijan taPresstv a nan Tehran tace, taron zai hada ministocin harkokin waje da manya manyan jami’an gwamnatin kasashe 57 na kungiyar indazasu tattauna kan al-amuran da suka shafi yankin da kuma duniya gaba daya.
Labarin ya kara da cewa, taron OIC a bagdaza shin a 52, kuma an sanya masa suna ‘tattaunawa da goyon baya, ginshikai ne masu muhimmanci na kawo zaman lafiya da ci gaba. ;.