A wani zaben jin ra’ayin da aka gudanar a kasar Faransa ya nuna cewa rabin musulmi a kasar Faransa sun ce zasu bar kasar Idan Le pen ta zama shugaban kasar Faransa.
Le pen wacce ita ce, shugaban Jam’iyyar National Rally (NR) mai tsananin kiyayya da musulmi da musulunci, ta bayyana a fili kan cewa idan aka zabeta a matsyin shugaban kasar Faransa to zata yaki abinda ta kira ‘masu ra’yin addinin Musulunci” daga ciki har da hana sanya hijabi a duk fadin kasar Faransa.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, za’a gudanar da zaben shugaban kasa a cikin watan Afrilun shekara ta 2027 mai zuwa. Kuma ga dukkan alamu, jam’iyyar NR ce zata lashe zaben.
Musulmi kimani 9,689 wadanda suka bayyana ra’ayin a zaben ‘French Institute of Public Opinion (IFOP) sun bayyana cewa idan jam’iyyar NR ta ci zabe suna tunanin zasu fice daga kasar Faransa. Don lallai musulmi ba zasu samun amince da zaman lafiya a karkashin ikonta ba.
A wasu zabubbukan jin ra’ayi, sakamakon ya nuna cewa Marine Le Pen zata zama shugaban kasar Faransa da kasha 81%. Sanan kimani kasha 1/4 na musulmi sun ce suna iya boye ikidarsu ta musulunci a lokacin shugabancinta.