IRGC : Tankar Mai Ta Yi Bindiga A Mashigar Hurmuz

Dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran IRGC bangaren Navy ko sojojin ruwa sun bada labarin cewa katafaren jirgin dakon man fetur dauke

Dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran IRGC bangaren Navy ko sojojin ruwa sun bada labarin cewa katafaren jirgin dakon man fetur dauke da ganga aklla miliyon biyu na danyen man fetur ya yi bindiga ya kuma maka da wuta a lokacinda ya yi karo da dakiya na karkashin ruwa a mashigar ruwa ta Hurmuz.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto majiyar IRGC na fadar haka a yau Asabar 17 ga watan Octoban shekara ta 2026. Ya kuma kara da cewa, Jirgin ya kashe na’urar GPS na gano inda yake, sannan ya dogara da jagoranci da kuma rakiyar sojojin Amurka CENCOM a lokacinda ya yi karo da nakiyar ya kuma kama da wuta.

IRGC NAVY basu bayyana sunan jirgin da inda ta wace kasa ba, amma ta kara da cewa sun yaudaru da sojojin CENCOM kafin su yi kokarin satar hanya na ficewa daga mashigar ruwan, al-ahali hukuma mai kula da mashigar ruwa da Hurmuz ta bukaci duk wanda ya ke son wucewa ta mashigar sai ya sami izinin wucewa.

Mashigar ruwa ta Hurmuz dai cikin kasar JMI, kuma a bude take har zuwa ranar 28 ga watan fabrayrun shekara ta 2026 da muke ciki, a ranar da sojojin Amurka da HKI suka farwa kasar da yaki daga ciki suka kashe Jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Imam shahid Aliyul Khaminaei da wasu daga cikin iyalan gidansa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted