An bude zaman Majalisar Ministocin Harkokin Waje ta Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulunci (OIC) karo na 52 a Bagadaza babban birnin kasar Iraki.
An bude zaman ne na kwanaki da taken “Tattaunawa da Hadin Kai: Ginshikai Biyu Masu Muhimmanci Don Inganta Zaman Lafiya da Ci Gaba Mai Dorewa.”
Ministan harkokin wajen Iran Abass Araghchi na daga cikin mahalarta taron.
Taron ya hada ministocin harkokin waje daga kasashen Musulunci 57 don tattauna muhimman batutuwan yanki da na kasa da kasa, da suka hada da batun Falasdinu da kuma kisan kare dangi da Isra’ila ke ci gaba da yi a Gaza.
“Iraki ta karbi shugabancin Majalisar Ministocin Harkokin Waje ta Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi daga hannun Turkiyya.
Kafin zaman taron, Sakatare Janar na OIC, Ismail Ould Cheikh Ahmed, ya jaddada cewa karuwar rikicin yanki da na duniya ya kara nauyin da ke wuyan kasashe mambobin kungiyar wajen karfafa zaman lafiya da hadin kan Musulmi.
Ya kuma yi kira da a dauki matakai da za su magance kalubalen da ake fuskanta a yanzu da kuma ci gaba da kokarin inganta hanyoyin aiki na kungiyar domin ta iya gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
Ana sa ran ajandar za ta kunshi abubuwan da ke faruwa a Falasdinu, yanayin jin kai da siyasa a fadin yankin, hadin gwiwar tattalin arziki, tsaron abinci, da kuma hadin gwiwa tsakanin kasashen mambobin kungiyar wajen magance kalubalen da aka samu.