An Yi Tattaunawar Farko Tsakanin ECOWAS Da Kasashen Sahel

Bangarorin biyu sun yanke shawarar bude tattaunawa kan hadin gwiwa a nan gaba.

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS da kuma kungiyar kasashen kawancen Sahel ta AES, sun yi tattaunawar keke da keke ta farko a tsakaninsu.

Tattaunawa ta farko tsakanin kungiyoyin ta faru ne a Senegal, bayan sanarwar ficewar Mali, Burkina Faso, da Nijar daga kungiyar a ranar 28 ga Janairu, 2024.

Bangarorin biyu sun yanke shawarar bude tattaunawa kan hadin gwiwa a nan gaba.

Tunda farko a taron da ministocin harkokin waje na kasashen uku na Kungiyar Kawacen Sahel sukayi a Ouagadoudou ya nuna cewa sun Magana da murya daya a lokacin tattaunawar da ECOWAS.

A cewar kasashen tattaunawar ba game da sake komwa ECOWAS ba ce, a’a, kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Burkina Faso Karamoko Jean Marie Traoré ya bayyana, game da “buɗe sabon babi don kafa sabuwar dangantaka” tsakanin kungiyar Kasashen Sahel da ECOWAS.

Hadin gwiwar tsaro, musamman a yaki da ta’addanci, ‘yancin zirga-zirgar mutane da kayayyaki, da kuma ci gaban tattalin arziki, zamantakewa, da shari’a suna daga cikin abubuwan da za a magance a yayin wadannan tattaunawar.

Manufar ita ce a fayyace sabbin tsare-tsare na hukumomi da na shari’a tsakanin Sahel Alliance da ECOWAS, tare da fifita muradun al’ummar Tarayyar, in ji ministocin harkokin wajen kasashen uku.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted