Tsohon shugaban ƙasar Senegal ya sanar a wannan Asabar, da janye takararsa ta neman mukamin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya.
A cikin wata sanarwa da aka buga a shafukan sada zumunta, Macky Sall ya ce ya yanke wannan shawara domin bayar da gudummawa ta cimma matsaya guda ta tsaida dan takara a Kwamitin Tsaro.”
Wannan dai na zuwa ne bayan da dukkan ‘yan takarar neman kujerar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya suka fuskanci suka daga membobin dindindin na Kwamitin Tsaro, wanda hakan ya bude kofa ga sabbin ‘yan takara.
“Sakamakon kuri’un gwaji daban-daban ya nuna fifiko ga ɗan takara daga yankin Latin Amurka da Caribbean, kuma wataƙila mace,” in ji tsohon shugaban ƙasar Senegal.
‘Yan takara bakwai a mukamin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya basu samu yabo ba daga membobin dindindin na Kwamitin Tsaro, wadanda ke da ikon hawa kujerar naki, a kuri’ar da wannan hukumar ta kada, a ranar Juma’a a cewar wata majiya ta diflomasiyya.
Kafafen yada labarai na Amurka sun bayyana cewa Washington tana adawa da dukkan ‘yan takaran bakwai da suka tsaya takarar.
Daga cikin jami’an diflomasiyya da ake ganin za su iya shiga akwai Nickolay Mladenov, babban wakilin Gaza a “Majalisar Zaman Lafiya” da Amurka ke marawa baya, da kuma Ministan Harkokin Waje na Hadaddiyar Daular Larabawa, Lana Nusseibeh.
An kuma ambaci sunan Feridun Hadi Sinirlioglu, Sakatare Janar na Kwamitin Tsaro da Hadin Kai a Turai (OSCE) ta Turkiyya.
Sauran ‘yan takarar su ne tsohuwar Ministan Harkokin Waje ta Guyana Carolyn Rodrigues-Birkett, Rafael Grossi na Argentina, shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) a yanzu, da Ivonne A-Baki na Ecuador, da Maria Fernanda Espinosa, da Olara Otunnu na Uganda.