Iran: Araqchi Ya Tattauna Da Takwarorinsa Na Oman Da Saudiyya

Ministan Harkokin Wajen Iran ya tattauna ta hanyar wayar tarho da ministocin harkokin wajen Oman da Saudiyya Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya sanar da yammacin jiya Litinin cewa ya yi shawarwari ta wayar tarho da ministocin harkokin waje na Oman, Badr al-Busaidi, da Saudiyya, Faisal bin Farhan. A yayin kiran biyu, Araqchi ya […]

Ministocin Harkokin Wajen Iran Da Japan Sun Tattauna Ta Wayar Tarho

An gudanar da tattaunawa ta hanyar wayar tarho tsakanin ministocin harkokin wajen Iran da Japan Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi da takwaransa na Japan, Toshimitsu Motegi, sun tattauna batutuwan da suka shafi bangarorin biyu da kuma sabbin ci gaban da aka samu a yankin gami da na kasa da kasa, musamman halin da yankin […]

Mohajerani: Iraniyawa 350 Ne Suka Yi Shahada A Yakin Baya-Bayan Nan

Mai magana da yawun gwamnatin Iran ta sanar da cewa: Ma’aikatan gwamnati sama da 350 ne suka yi shahada a lokacin yaki kan kasar Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatimah Mohajerani ta sanar da cewa: Ma’aikatan gwamnatin kasar sama da 350, wadanda suka yi wa mutane hidima a sassa daban-daban, suka yi shahada a […]

Iran: Killace Mashigar Hormuz Yana Nufin Faɗaɗa Matakin Yaƙi Ne

Hedikwatar Rundunar Sojin Khatamal- Anbiya ta Iran ta jaddada cewa: Killace yankin mashigar Ruwan Hormuz yana nufin faɗaɗa matakin yaƙi ne Hedikwatar Rundunar Sojin Khatamal-Anbiya (Alaihissalam) ta fitar da wata sanarwa a ranar Litinin tana nuni da cewa: Ci gaba da munanan ayyukan Amurka, musamman ayyukanta na kawo cikas a yankin, da kuma sanya takunkumin […]

Wani Ba’amurke Ya Dirar Mikiya Kan Fira Ministan Isra’ila

Wani ɗan wasan kwaikwayo ɗan Amurka ya yi diran mikiya kan fira ministan Isra’ila yana siffanta shi da “Mai kisan kai da ba zai tsira daga fuskantar shari’a ba Jarumin fina-finai na Amurka Mark Ruffalo ya kai hari ga Fira Ministan gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu, yana mai kiransa da “mai tabin hankali na […]

Hare-haren Yemen Sun Dakatar Da Ayyukan Babbar Matatar Mai Ta Saudiyya

hotunan tauraron dan'adam akan matatar man Saudiyya

Kamfanin tace man fetur na Aramco dake yankin Buqiq a Saudiyyaya dakatar da ayyukansa bayan hari da jirgi maras matuki daga kasar Yemen. Hotunan tauraron dan’adam na kamfanin “Santinel 2” ya bayana barna mai yawa da aka yi wa masana’antar dake tura man fetur ta bututu daga yammaci zuwa gabashin Saudiyya,a yankin Buqiq.Hotunan sun nuna […]

Amurka: Man Fetur Na Tsumi Ya Ragu Fiye Da Kowane Lokaci A Baya

Matatar Man Fetur

A wani bayani da hukumar makamashi ta kasar Amurka ta fitar ta bayyana cewa makamashin ajiyar da kasar take da shi, ya sami koma baya da ganga miliyan 3.7 a cikin mako daya kadai, da hakan ya sa jumillar wanda aka rage ya kai ganga miliyan miliyan 307.7. Sanarwar ta ce rabon da a ga […]

Baqa’i: Iran Ba Zata Bari Amurka Ta Tantance Lokacin Yaki Da Zaman Lafiya Ba

A lokacin ganawarsa da manema labarai a birnin Tehran a jiya litinin kakakin ma’aikatar harkokin waje na kasar iran Isma’ila Baqa’I da yake amsa tambayar da aka yi masa game da matsayar iran da Amurka ga kasar Pakistan da Qatar na shirin tattaunawa don kawo karshen yaki kan iran, “yace ban san yadda kuke ganin […]

Iran: Bukatun Amurka Kan Tattaunawar Sun Wuce Iyaka

A wani bayani da mataimakin ministan harkokin wajen kasar iran Kazeem Garibabadi yayi  game da tattaunawar da ake yi tsakaninsu da Amurka a birnin Islam abad na kasar Pakistan , yace iran tayi watsi da bukatar da bangaren Amurka ta gabatar saboda ya yi yawa sosai da ya wuce iyaka. Ya kara da cewa bangaren […]

Gaza: Falasdinawa 3 Sun yi Shahada A Hare-haren Isra’ila

Rahotanni sun bayyana cewa falasdinwa 3 sun yi shahada yayin da wasu 15 kuma suka jikkata a jiya litinin sakamakon hari da sojojin Isra’ila suka kai a a yankuna daban-daban a yankin Gaza, a cigaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da suke yi da aka cimma tun ranar 10 ga watan Oktoban shekarar […]