A wani bayani da hukumar makamashi ta kasar Amurka ta fitar ta bayyana cewa makamashin ajiyar da kasar take da shi, ya sami koma baya da ganga miliyan 3.7 a cikin mako daya kadai, da hakan ya sa jumillar wanda aka rage ya kai ganga miliyan miliyan 307.7.
Sanarwar ta ce rabon da a ga koma baya irin wannan tun 1983.
Amurkan dai ta bayar da umarnin a yi amfani da gangar man fetur miliyan 172 daga wanda take tsumi saboda rage hauhawar farashinsa a kasuwanninta na cikin gida.
Amurkan dai ta jefa kanta cikin wannan matsalar ne saboda yakin da ta kallafawa Iran da ya kai ga rufe mashigar ruwan Hurmuz.