Kamfanin tace man fetur na Aramco dake yankin Buqiq a Saudiyyaya dakatar da ayyukansa bayan hari da jirgi maras matuki daga kasar Yemen.
Hotunan tauraron dan’adam na kamfanin “Santinel 2” ya bayana barna mai yawa da aka yi wa masana’antar dake tura man fetur ta bututu daga yammaci zuwa gabashin Saudiyya,a yankin Buqiq.Hotunan sun nuna yadda bakin hayani yake tashi daga wajen bayan kai harin.
Daga wannan wurin ne dai Saudiyya take bai wa duniya kaso 7% na jumillar man fetur.
A jiya Litinin da marece ne dai sojojin kasar Yemen su ka sanar da kai hari akan batutun jigilar man fetur a gabashin Saudiyya wanda yake hada yankin “Luwailah” ba tare da ya bi ta mashigar ruwan Hurmuz ba.
Hotunan dauraron dan’adam na hukumar sararin samaniya ta Amurka “Nasa” ya nuna tashin gobara a cikin wannan cibiyar da daya ce daga cikin masu bai wa duniya man fetur.
Kasar Yemen dai ta sanar da cewa, matukar Saudiyya tana kai mata hari, to kuma za ta mayar da martani. Gwamnatin ta Sanaa tana son ganin Saudiyyar ta dauke takunkumin da ta kakaba mata ne ta ruwa da sama, tana mai shelanta nata takunkumin akan jiragen ruwa Saudiyya.
Shekaru 11 kenan da Saudiyya ta kakaba wa Yemen takunkumi ta sama da kuma ruwa da hakan yake shafar tattalin arziki da kuma rayuwar mutane ta yau da kullum.