Karbala: Akalla Iraniyawa Miliyan 6 Ne Za Su Halarci Tattakin Arbaeen

Da akwai alakar 'yan'uwantaka wacce take tsakanin al'ummar Iraki da Iran tana a matsayin manuniya akan za a yi wa maziyartar kyakkyawan fatan na mutanen
ziyarar Arba'in

Hukumar alhazai da Ziyara ta Iran, ta bayyana cewa ana sa ran cewa adadin Iraniyawan da za  su shiga cikin kasar Iraki domin yin ziyarar 40 ta shahadar Imam Hussain (a.s) za su kai miliyan 6.

 Wakilin hukumar aikin haji da ziyarar na Iran a kasar Iraki Muhsin Isma’il Sagarji a fada wa kamfanin dillancin labarun Iraqi ( Wa’a) cewa; “Da akwai alakar ‘yan’uwantaka wacce take tsakanin al’ummar Iraki da Iran tana a matsayin manuniya akan za a yi wa maziyartar kyakkyawan fatan na mutanen da ake hasashen cewa za su kai miliyan 6.”

Haka nan kuma ya ce; Da akwai kungiyoyi na masu hidima daga Iran da za su kai 3,000 da za su yi aiki a cikin haromomi masu tsarki.”

 A baruruwan Najfa da Karbala, mahukunta sun yi alkawalin warewa tawagogin Iraniyawa man fetur da ababen hawansu  suke bukatuwa da su, haka nan sauran kayan aikin da za su bukatu da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted