A lokacin ganawarsa da manema labarai a birnin Tehran a jiya litinin kakakin ma’aikatar harkokin waje na kasar iran Isma’ila Baqa’I da yake amsa tambayar da aka yi masa game da matsayar iran da Amurka ga kasar Pakistan da Qatar na shirin tattaunawa don kawo karshen yaki kan iran, “yace ban san yadda kuke ganin za su ci gaba da yakin ba , yakin da ake tsammanin zai tilastawa iran ta mika wuya, sai gashi sun makale cikin mawuyacin hali tsawon watanni 5. suna ta fadi tashi a cikin wani yanayi da su suka samar da shi tare da gwamnatin isra’ila
Baqai ya kara da cewa abin da yake da muhimmancin a wajensu shi ne muradun kasa, shawarwari kan lamuran kasa ba za su yi daidai da abubuwan da baa sani ba, abin da yafi muhimmanci garemu shi ne tsaron iran da kuma muradun kasa, kuma ana yanke matsaya game da ita ne ta hanyar wani tsari na musamman
Yace muna su mu ce ba zamu bari Amurka ta zama ita za ta tantance lokacin yaki da kuma lokacin zaman lafiya ba, zamu ci gaba da kare kan mu gwargwadin yadda yanayi ya bayar
Kasar Amurka da Isra’ila sun kaddamar da haramtaccen yaki kan kasar iran tun a ranar 28 ga watan fabareru, sai dai bayan kwanaki 40 a ranar 8 ga watan Aprilu an tilastawa makiya amincewa da dakatar da bude wuta a daidai lokacin da iran take nuna jajircewa da samun nararori wajen mayar da martani
A ranar 17 ga watan yuni kuma Tehran da Washington sun rattaba hannu kan yarjejeniyar islamabad ta kawo karshen yaki da fara tattaunawa, sai dai Washington ta keta dukkan abubuwan da aka cimma a yarjejeniyar da suka sanya iran ta mayar da martani mai gauni