Iran Ta yi Watsi Da Bukatun Da Amurka Ta Gabatar A Tattaunawar Da Ake yi Saboda Sun Wuce Iyaka

A wani bayani da mataimakin ministan harkokin wajen kasar iran Kazeem Garibabadi yayi  game da tattaunawar da ake yi tsakaninsu da Amurka a birnin Islam

A wani bayani da mataimakin ministan harkokin wajen kasar iran Kazeem Garibabadi yayi  game da tattaunawar da ake yi tsakaninsu da Amurka a birnin Islam abad na kasar Pakistan , yace iran tayi watsi da bukatar da bangaren Amurka ta gabatar saboda ya yi yawa sosai da ya wuce iyaka.

Ya kara da cewa bangaren Amurka sun sanar cewa idan baa amince da bukatun da suka gabatar ba, ya nuna ke nan tattaunawar ba tayi nasara ba, za su tafi su bar tattaunawar, kuma abin da ya faru ke nan bayan da iraniyawa suka ki amincewa da bukatunsu sai suka fice daga tattaunawar.

Da yake Magana game da ci gaban da aka samu kan mashigar Hurmuz yace bayan da kasar iran ta sake rufe mashigar hurmuz biyo bayan laifukan da Amurka ta tafka, aka fara gudanar da tattaunawa a kasar Oman kusan makwanni 2 da suka gabata

Daga kareshe ya ce mun riga mun sanar cewa  duk yadda sakamakon tattaunawar ya kasance manufofin kasar iran tun farkon fara yakin a bayyaane yake, don haka ba zaa amince da wadannan shawarwari ba, don haka siyasar ci gaba da rufe mashigar hurmuz da killacewar da aka yi ma jiragen ruwa a teku za ta ci gaba da gudana, wanda wannan wani samfuri ne na diplomasiyar kasar iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted