Falasdinawa 3 Ne Suka yi Shahada Sakamakon Hare-haren Da HKI Ta Kai A Yanki Gaza

Rahotanni sun bayyana cewa falasdinwa 3 sun yi shahada yayin da wasu 15 kuma suka jikkata a jiya litinin sakamakon hari da sojojin Isra’ila suka

Rahotanni sun bayyana cewa falasdinwa 3 sun yi shahada yayin da wasu 15 kuma suka jikkata a jiya litinin sakamakon hari da sojojin Isra’ila suka kai a a yankuna daban-daban a yankin Gaza, a cigaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da suke yi da aka cimma tun ranar 10 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata ta 2025

A garin jabaliya dake arewacin gaza sojojin isra’ila sun kashe bafalasdine guda tare da jikkata wasu guda 3, kamar yadda majiyar lafiya ta bayyana, a garin khan yunus ma wani matashi bafalasdine yayi shahada wasu da dama kuma sun jikkata a kusa da gadar karara dake arewacin garin

Har ila yau wasu falasdinawa guda 3 sun yi shahada ciki har da wata mace matashiya, a wani samame da sojojin Isra’ila suka kai a sansanin falasdinawa yan gudun hijira dake yankin maslakh turki a kudancin khan yunus, shi ma wani bafalasdine ya jikkata bayan da sojojin isra’ila suka bude masa wuta a khan yunus.

A yankin Gaza jiragen ruwan isra’ila sun bude wuta kan wasu masunta a lokacin da suke gudanar da ayyukansu a gabar ruwan garin, bayan da jiragen ruwa na yaki na Isra’ila suka tunkarosu sai suka bude musu wuta, kamar yadda shedun gani da ido suka shaidawa manema labarai

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted