Wani Dan Kasar Amurka Ya Dirar Mikiya Kan Fira Ministan Isra’ila

Wani ɗan wasan kwaikwayo ɗan Amurka ya yi diran mikiya kan fira ministan Isra’ila yana siffanta shi da “Mai kisan kai da ba zai tsira

Wani ɗan wasan kwaikwayo ɗan Amurka ya yi diran mikiya kan fira ministan Isra’ila yana siffanta shi da “Mai kisan kai da ba zai tsira daga fuskantar shari’a ba

Jarumin fina-finai na Amurka Mark Ruffalo ya kai hari ga Fira Ministan gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu, yana mai kiransa da “mai tabin hankali na kisan kai,” bayan Netanyahu ya yi maraba da korar mai shigar da kara na Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya Karim Khan.

A wani rubutu da ya yi a dandalinsa na X-rated a ranar Litinin, Ruffalo, mai shekaru 59 a duniya, ya ce korar mai shigar da kara na kotun ICC ba zai goge laifukan yaki da Haramtacciyar kasar Isra’ila ta aikata a Zirin Gaza ba.

Ya kara da cewa, “Netanyahu ba zai tsere wa shari’a ba, kuma ba zai iya canza tarihi ba. Shi mai tabin hankali ne na kisan kai, kuma haka tarihi zai tuna da Benjamin Netanyahu a koda yaushe.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted