Iraniyawa 60 ne suka yi shahada wasu guda 670 kuma sun jikkata a kudancin kasar

Ministan kula da  kiwon lafiya na kasar iran ya bayyana cewa kimanin mutane 60 ne suka yi shahada  yayin da wasu guda 670 kuma suka

Ministan kula da  kiwon lafiya na kasar iran ya bayyana cewa kimanin mutane 60 ne suka yi shahada  yayin da wasu guda 670 kuma suka jikkata  sakamakon hare-haren da kasar Amurka ta kai a kudancin kasar a cikin kwanaki 10 zuwa 12 da ta sake kaddamar da yaki kan kasar

Kasar Amurka ta kaddamar da hare-hare a kasar iran a cikin kwanaki da suka gabata , inda suka mayar da hankali wajen kai hare-hare a yankunan dake kudancin kasar,kuma sun hari gadoji da wasu muhimman wurare na amfanin Alumma.

A matsayin matakin mayar da martani dakarun sojin kasar Iran sun kaddamar da hare-hare a sansanonin Amurka dake yankin, a kasashen tekun fasha da jodan, da kuma siriya, kuma sun kai hari kan muhimman wurare dake da alaka da kasar Amurka.

Wani da rahoto da kamfanin dillancin labarai na reuters nakalto ya nuna cewa mutum daya cikin mutane 3 a Amurka ne yake goyon bayan yakin da Trump ya kaddamar kan kasar Iran, inda mafiyawanci basa goyon bayan yakin da aka fara tun  watanni biyar da suka gabata

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted