Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Iran Da Japan Sun Tattauna Ta Hanyar Wayar Tarho

An gudanar da tattaunawa ta hanyar wayar tarho tsakanin ministocin harkokin wajen Iran da Japan Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi da takwaransa na Japan,

An gudanar da tattaunawa ta hanyar wayar tarho tsakanin ministocin harkokin wajen Iran da Japan

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi da takwaransa na Japan, Toshimitsu Motegi, sun tattauna batutuwan da suka shafi bangarorin biyu da kuma sabbin ci gaban da aka samu a yankin gami da na kasa da kasa, musamman halin da yankin ke ciki a yanzu, a wata tattaunawa ta wayar tarho a ranar Talata da rana.

A yayin kiran, Araqchi ya yi wa takwaransa na Japan bayani game da sabbin ci gaban da aka samu game da kokarin diflomasiyya da nufin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Dukan bangarorin biyu sun jaddada bukatar ci gaba da hadin kai da hadin gwiwa don magance kalubalen tsaro da Amurka ta sanya a mashigar tekun Hormuz sakamakon hare-haren wuce gona da iri da take kai wa.

Ministocin harkokin wajen Iran da Japan sun kuma yi musayar ra’ayoyi kan wasu batutuwa da dama na ofishin jakadancin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted