Kakakin Gwamnatin Iran Ta Ce: Iraniyawa 350 Ne Suka Yi Shahada A Yakin Baya-Bayan Nan

Mai magana da yawun gwamnatin Iran ta sanar da cewa: Ma’aikatan gwamnati sama da 350 ne suka yi shahada a lokacin yaki kan kasar Mai

Mai magana da yawun gwamnatin Iran ta sanar da cewa: Ma’aikatan gwamnati sama da 350 ne suka yi shahada a lokacin yaki kan kasar

Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatimah Mohajerani ta sanar da cewa: Ma’aikatan gwamnatin kasar sama da 350, wadanda suka yi wa mutane hidima a sassa daban-daban, suka yi shahada a lokacin yaki kan Iran.

Mohajerani ta lura cewa filin jirgin saman Bushahr ya daina aiki kwata-kwata kuma yana bukatar sake ginawa, ta kara da cewa wani jirgin sama da aka saya don amfanin jama’a a filin jirgin ya samu matsala saboda hari da ya fuskanta da makami mai linzami.

Ta ci gaba da cewa a lokacin wadannan hare-haren, an lalata gadoji 12 da hanyoyin shiga harabal otal guda biyu.

Mohajerani ta bayyana cewa gwamnati za ta karfafa karfin tsaronta ta kowace hanya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted