Kungiyoyi Masu Gwagwarmaya Sun Yi Tir Da HKI Saboda Hare-haren Beirut

Kungiyoyi da kasashe masu gwagwarmaya a yammacin Asiya sun yi allawadai da hare-haren da HKI ta kai unguwar Dhahiya Junubiyya na birnin Beirut babban birnin

Kungiyoyi da kasashe masu gwagwarmaya a yammacin Asiya sun yi allawadai da hare-haren da HKI ta kai unguwar Dhahiya Junubiyya na birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon a jiya Lahadi da yamma wanda ya kai ga shahadar mutane 5 da kuma raunata wasu 28. Daga cikin wadanda suka yi shahada har da babban kwamandan kungiyar Hizbullah Shahid Ali Tabatabai.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyoyi da kasashen da suka yi allawadai da hare-haren kamar haka. Akwain kungiyoyin Falasdinawa masu gwagwarmaya wadanda suka hada da Hamas, Jihadul Islami, PFLP, kungiyar falasdinawa masu gwagwarmaya (PMM), Ansarullah mai gwagwarmaya.

Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen JMI da kungiyoyi masu gwagwarmaya a kasar Iraki duk sun yi allawadai da hare-haren sun kuma dorawa Amurka laifukan abinda HKI take aikatawa a yankin yammacin Asiya.

Dr Ali Larijani sakararen majalisar koli da tsaron kasar Iran ya yi tira da hare-haren na birnin Beirut ya kuma aza laifin kan shugaban kasar Amurka Donal Trump wanda yake bawa HKI goyon baya 100% kan abinda take aikatawa a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted