Amnesty International Ta Zargi Najeriya Da Gazawa Wajen Kare Rayukan Al’ummarta

Ƙungiyar kare hakkin Dan adam ta Amnesty International ta zargi gwamnatin Najeriya da gaza kare yara kanana a fadin kasar, yayin da ake ci gaba

Ƙungiyar kare hakkin Dan adam ta Amnesty International ta zargi gwamnatin Najeriya da gaza kare yara kanana a fadin kasar, yayin da ake ci gaba da samun karuwar hare-hare da sace-sacen mutane da ake kai wa wasu makarantu a arewacin kasar.

Amnesty ta ce ta na nuna damuwa akan yadda gwamnatin Najeriya ke kara nuna gazawa a wajen kare rayukan mutane da dukiyoyinsu musamman ma yara ‘yan makaranta.

Isa Sanusi, shi ne daraktan kungiyar ta Amnesty International a Najeriya, ya shaida wa manema labarai cewa, abin da ke faruwa yanzu ya nuna cewa ilimi zai kara samun koma fiye da baya, sai dai bisa ga yadda abubuwa ke faruwa a yanzu na rashin tsaro da satar dalibai abin zai kara yin kamari.

Ya ce,” Rufe-rufen makarantu da ake yi yanzu a arewacin Najeriya, wasu yaran har abada ba za su koma makaranta ba, don haka mu muna gani wannan babban bala’i ne don haka ya kamata gwamnati ta tashi tsaye ta yi abin da ya dace.”

Isa Sanusi, ya ce,”Aikin gwamnati ba wai shi ne gina kwalta gina gadar sama bane, kare dukiya da rayukan mutane shi ne abin da ya rataya a wuyan gwamnati kuma ta gaza akansa.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments