Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon na juyayin shahadar kwamanda haitham Ali Al-tabataba’i da aka fi sani da Abu Ali wanda yayi shahada tare da wasu dakarun hizbullah guda 4 a wani mummunan hari da Isara’ila ta kai a heret hareik dake kudancin birnin berut na kasar labanon.
Tabataba’I yana daya daga cikin jajircaccen dakarun kungiyar hizbullah , kuma ya taka rawa sosai wajen tsarin tsaron kungiyar tun shekarun farko da aka kafata, kisan nasan ya kara nuna irin yadda isra’ila ke keta yarjejeniyar dakatar da tsagaita bude wuta da aka cimma, kuma kisan nasa zai kara karfafa jajircewa a turbar gwagwarmaya a yankunan labanon da falasdinu.
Kungiyar hizbullah ta bayyana cewa babban kwamandan ya bi dan uwansa da yayi shahada bayan daukar dogon lokaci na neman samun shahada inda ya sadaukar da rayuwarsa wajen gwagwarmaya da jajircewa.
A yamacin jiya lahadi ce isra’ila ta kai hari a gidansa da ke kudancin labanon inda tayi kashe mutane 5 tare da jikkata wasu guda 28 kuma ya lalata shaguna da gidaje dake makwabtaka da shi .