A dare na uku na makokin shahadar Fatiman Azzahra (s) diyar manzon All.. (s) shuwagabannin bangarorin gwamnati 3 a nan Iran sun sami halattan makakinta (s) a Husainiyyar Imam Khomanin(q) dake nan Tehran.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa, shugaban kasa Dr Masoud Pazeshkiya, Alkalin alkalai Hujjatul Islam Sheikh Ibrahim Ijeyi da kuma Muhammad Bakir Qalibaf sun sami halattan taron makoki da ta’ayin Zahra, wanda Hujjatul Islam Nasir Rafi’ii ya karanta.
A cikin jawabinda a zaman makokin Rafi’ii ya yi maganar Jagoranci, da kuma yadda Zahra (s) ta yi amfani da ragowar rayuwarta dan kadan bayan shahadar Mahaifinta don assasa wata harka ta goyon bayan hakkin mijinta kuma shugabanta Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib(a). Harka wanda zai wanzo har duniya ta nade.
A ranar irin ta yau ce 3 ga watan Jamada Thani, Zahra (s) ta yi shahada makonni kadan bayan shahadar mahaifinta manzon All..(s). saboda matsalolin da ta faskanta da sabbin shuwagabanni bayan mahaifinta.