Habasha: Bayan Shekaru 10,000 Dutsen Hayli Gubbi Ya Yi Aman Wuta

Rahotanni daga kasar Habasha sun ce dutsen na Hayli Gubbi ya fitar da kura da toka mai yawa da ta shiga kasashen Oman da Yemen.

Rahotanni daga kasar Habasha sun ce dutsen na Hayli Gubbi ya fitar da kura da toka mai yawa da ta shiga kasashen Oman da Yemen.

Masana ilimin kasa sun ce lokaci na karshe da dutsen ya yi aman wuta shi ne shekaru 10,000 da su ka gabata. Bugu da kari, masana ilimin kimiyya sun ce abinda ya faru yana da jan hankali bisa la’akari da cewa a ya dade bai yi amanwuta ba.

Shi dai dutsen Hayli Gubbi yana da nisa kilo mita 15 daga dutsen Etra Ali wanda shi ma yana yin aman wuta.

Yankin da lamarin ya faru wanda ake kira da “Dankali”yana daga cikin wuraren da su ka fi tsananin zafi a duniya da ba kasafai bil’adama kan rayu a cikinsu ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments