A sanarwar da kungiyar ta Hizbullah ta fitar a jiya Lahadi ta ce; “A cikin dukkanin alfahari Hizbullah tana sanarwa da ‘yan gwgawarmaya da al’ummar Lebanon, shahadar babban kwamanda na jihadi Shahid Haisam Ali Tabtaba’i ( Sayyid Abu Ali) wanda ya yi shahada sanadiyyar harin wuce gona da iri na yaudara na Isra’ila a yankin Harrik dake unguwar Dhahiya a kudancin Lebanon.”
Sanarwar ta kuma kara da cewa; Shahidin ya hade da ‘yan’uwansa shahidai bayan tsawon lokaci na jihadi,gaskiya, kyakkyawar niyya da tsayin daka akan tafarkon gwgawarmaya da aikin da babu kakkautawa wajen fuskantar abokan gaba har zuwa lokaci na karshe na rayuwarsa.”
Haka nan kuma sanarwar ta ci gaba da cewa; Shahidin yana cikin wadanda kafa harsashin gwgawarmaya saboda ta ci gaba da zama cikin karfi ta kare kasa da kuma sami nasarori.”
Shi dai Shahid Tabtaba’i an haife shi ne a 1968 ya kuma rike mukamai mabanbanta na soja a karkashin gwgawarmayar musulunci. Tun daga kafa kungiyar Hizbullah a 1982 ne yake a cikinta, ya kuma halarci horo na soja a lokuta mabanbanta. Bayan yakin taimakawa Gaza ” Ulul-Ba’as” ya zama kwamandan mayakan Hizbullah.
Tun da fari ma’aikatar lafiya a Lebanon ta ce mutum biyar ne suka rasa rayukansu a wani sabon harin Isra’ila a Kudancin babban birnin Kasar, inda kuma ta raunata kimanin fararen hula 28.