Mutane 6 Ne Suka Mutu Sakamakon Harin Kunar Bakin Wake Da Aka Kai A Peshavar Na Kasar Pakistan

Rahotanni sun bayyana cewa an kai harin bakin wake a hedkwatar FC dake peshavar na kasar Pakistan da safiyar yau kuma yayi sanadiyar mutuwar mutane

Rahotanni sun bayyana cewa an kai harin bakin wake a hedkwatar FC dake peshavar na kasar Pakistan da safiyar yau kuma yayi sanadiyar mutuwar mutane 6, da ya hada da jamian tsaro 3 da kuma wasu guda 3 na daban, wannan shi ne hari mafi muni da aka kai kan jami’an tsaro a kasar Pakistan a wannan watan.

Wannan harin yana nuna irin matsalar tsaro da kasar Pakistan ke fuskanta adaidai lokacin da ake samun karuwar ayyukan yan ta’adda daga kungiyar tehrik e Taliban TTP  wadda Islamabad ke zarginta da gudanar da ayyuka a boye akan iyakar Afghanistan.

Ana sa bangaren fira ministan kasar Pakistan Shehbaz sharif yayi tir da kai harin , kuma ya bukaci gudanar da bincike don gano wadanda ke da hannu wajen kai harin tare da gurfanar da su a gaban kuliya manta sabo

Shi ma shugaban kasar Asif Ali Zardari ya yi Allah wadai da kai harin kamar yadda ya rubata a shafinsa na X kuma ya aike da ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu ,kuma yace wannan zai karawa jamian tsaron kasar karfin guiwa ne da jajaircewa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted