Shugaban Kasar Iran Ya Ce: Ba Za Su Kyale A Lalata Alakar Iran Da Armeniya Ba

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Ba za su ƙyale kowa ya lalata dangantakar abokantaka da ke tsakanin Iran da Armeniya ba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, yayin ganawarsa da Armen Grigoryan, sakataren kwamitin tsaron kasar Armeniya a yau Asabar, ya jaddada cewa: Dole ne su tabbatar da cewa babu wani karfin kasashen waje da […]

Kasar Denmark Tana Goyon Bayan Dakatar Da Yarjejeniyar Kasuwacin Da Isra’ila

Gwamnatin kasar Denmark ta sanar da cewa: Tana goyon bayan dakatar da yarjejeniyar kasuwanci da haramtacciyar kasar Isra’ila Ministan harkokin wajen Denmark Lars Løkke Rasmussen ya fada a ranar Asabar cewa: Kasarsa tana goyon bayan dakatar da yarjejeniyar kasuwanci da haramtacciyar kasar Isra’ila da nufin kawo karshen yakin Gaza. Ya kara da cewa: Abin da […]

Moroko: Zanga-Zangar Rashin Amincewa Da Kisan Kiyashi Da Kakaba Yunwa A Gaza

Zanga-zangar adawa da kakaba yunwa da gudanar da kisan kare dangi da sojojiin mamayar Isra’ila ke yi a Gaza a biranen kasar Morocco Dubban al’ummar Moroko ne suka gudanar da zanga-zanga a garuruwa da dama na masarautar kasar a cikin jerin gwanon dare, domin neman kawo karshen yunwa da kisan kiyashin ga Falasdinawa a zirin […]

Guinea: An Fara Tattaunawa Kan Zaben Raba Gardama Na Sabon Kundin Tsarin Mulki

A wannan makon ne aka bude damar tattauna na kowa da kowa a kasar Guinea dangane da zaben raba gardama na sabon kundin tsarin mulkin kasar. Shafin yanar gizo na labarai Africa News ya bayyana cewa gwamnatin rikon kwarya na kasar ya bayyana cewa tattaunawa kan sabon kundin tsarin mulkin kasar zai gudana ne a […]

Turkiyya Ta Bukaci A Dakatar Da Isra’ila (HKI) Daga Majalisar dinklin duniya

Majalisar dokokin kasar Turkiyya ta yi tir da kissan kiyashin da HKI take aikatawa a Gaza sannan ta amince da hana jiragen fisinja na HKI wucewa ta sararin samaniyar kasar. Banda haka ta bukaci a kore daga Majalisar dinkin duniya. Majalisar ta bukaci a kula da hakkin Falasdinawa a fagen kasashen a kuma kawo karshen […]

Iran: IRGC Sun Kama Ma’aikatan Mosad A Arewa Maso Gabacin Kasar

Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran sun bada labarin kama ma’aikatan Mosad na HKI a lardin Khorasan Razavi  da ke arewa maso gabacin kasar, wadanda suka taimakawa HKI a kan hare-haren da ta kaiwa kasar na kwanaki 12 a cikin watan Yunin da ya gabata. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran […]

Iran Ta Yi Watsi Da Shirin ‘SnapBack’ Na Kasashen Turai

Jakadan kasar Iran a majalisar dinkin duniya Amir Saeed Iravani yayi watsi da shirin kasashen turai 3 na sake farfado da takunkuman MDD kan Iran.. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Iravani yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa  Iran tana kan bakanta na tattauna da wadan nan […]

E3 sun gindaya sharudda 3 kan dakatar da dawo da  takunkuman MDD a kan Iran

A ranar Juma’a ne Birtaniya da Faransa da Jamus suka gindaya wasu sharudda guda uku ga Iran game da batun dage mayar da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya a kanta,a  cikin wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar gabanin wani taron sirri na kwamitin sulhu na MDD. Kasashen uku da aka fi sani da E3  sun […]

Amurka ta hana izinin shiga kasarta ga shugaban Falastinawa don halartar taron MDD

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar a jiya Juma’a cewa, sakataren harkokin wajen kasar Marco Rubio ya yanke shawarar  soke takardar izinin shiga kasar ga wasu mambobin kungiyar ‘yantar da ‘yancin Falasdinu (PLO) da hukumar Falasdinu (PA), ciki har da shugaban PA Mahmoud Abbas, gabanin taron shekara-shekara na Majalisar Dinkin Duniya da za a yi […]

Rwanda ta dauki bakin haure kashi na farko da aka kora daga Amurka

Cibiyar Bloomberg ta bayar da rahoton cewa, Rwanda ta karbi  rukunin farko na bakin haure da aka kora daga Amurka, a karkashin wata yarjejeniya mai cike da takaddama tsakanin gwamnatin kasar da  gwamnatin Donald Trump. Mai magana da yawun gwamnatin Rwanda  Yolande Makolo ya tabbatar da cewa “rukunin farko na bakin haure bakwai da aka […]

Mali: Kungiyar Al-Qaeda ta kwace iko da garin Farabougou da ke tsakiyar kasar

Shugaban mulkin sojin Mali Janar Asimi Goita

Mayakan ‘Yan ta’adda na  kungiyarAl-Qaeda sun karbe ikon garin Farabougou da ke tsakiyar kasar Mali, mako guda bayan da suka kwace sansanin sojojin da ke garin, a cewar kamfanin dillancin labaran Faransa. Kungiyar ‘yan ta’adda ta (JNIM) ta sanar a wasu jerin sakonni da ta fitar cewa,  ta kwace garin tare da kafa abin da […]