Shugaban Kasar Iran Ya Ce: Ba Za Su Kyale A Lalata Alakar Iran Da Armeniya Ba

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Ba za su ƙyale kowa ya lalata dangantakar abokantaka da ke tsakanin Iran da Armeniya ba Shugaban kasar Iran

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Ba za su ƙyale kowa ya lalata dangantakar abokantaka da ke tsakanin Iran da Armeniya ba

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, yayin ganawarsa da Armen Grigoryan, sakataren kwamitin tsaron kasar Armeniya a yau Asabar, ya jaddada cewa: Dole ne su tabbatar da cewa babu wani karfin kasashen waje da zai iya wargaza dangantakar abokantaka tsakanin Iran da Armeniya.

Shugaba Pezeshkian ya jaddada cewa, damuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da abubuwan da ke faruwa a yankin Caucasus na baya-bayan nan, musamman kasancewar dakarun kasashen waje a wannan yanki mai matukar muhimmanci, an kawar da su sosai bisa la’akari da fayyace da kuma tabbacin da jami’an kasar Armeniya suka bayar. Ya ce, “Dole ne su yi aiki ta hanyar da babu wani ikon kasashen waje da zai iya lalata dangantakar abokantaka da dabarun da ke tsakanin kasashen biyu.”

Shugaban na Iran ya ci gaba da nuna jin dadinsa da aiwatar da aikin hanyar Arewa da Kudu, inda mahukuntan kasar Armeniya suka mai da hankali kan wannan lamari. Ya dauki matakin kammala wannan aiki a matsayin wani muhimmin mataki na karfafa cudanya a fannin tattalin arziki da ma siyasa a tsakanin kasashe mambobin kungiyar Eurasia, yana mai jaddada cewa: gaggauta aiwatar da yarjejeniyoyin kasashen biyu, musamman a fannin zirga-zirga tsakanin Iran da Armeniya, na daya daga cikin muhimman nasarorin wannan ziyara, kuma daya daga cikin fitattun sakamakon tuntubar juna da manyan jami’an kasar Armeniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments