Mali: Kungiyar Al-Qaeda ta kwace iko da garin Farabougou da ke tsakiyar kasar

Mayakan ‘Yan ta’adda na  kungiyarAl-Qaeda sun karbe ikon garin Farabougou da ke tsakiyar kasar Mali, mako guda bayan da suka kwace sansanin sojojin da ke

Mayakan ‘Yan ta’adda na  kungiyarAl-Qaeda sun karbe ikon garin Farabougou da ke tsakiyar kasar Mali, mako guda bayan da suka kwace sansanin sojojin da ke garin, a cewar kamfanin dillancin labaran Faransa.

Kungiyar ‘yan ta’adda ta (JNIM) ta sanar a wasu jerin sakonni da ta fitar cewa,  ta kwace garin tare da kafa abin da ta kira tsarin shari’a musulunci.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya nakalto wasu jami’an yankin da suka tsere daga Farabougou na cewa yanzu haka garin na karkashin ikon kungiyar JNIM.

A makon da ya gabata ne aka tilastawa sojojin ficewa daga sansaninsu da ke Farabougou, daya daga cikin sansanoni mafi girma a yankin, bayan wani hari da mayakan masu ikirarin jihadi suka kai musu.

Tun daga wancan lokaci sojojin ba su yi wani yunkuri  na shiga garin ba domin sake kwato shi daga hannun ‘yan ta’adda. Sai dai hukumomi sun tabbatar da kai harin na ‘yan ta’adda, amma ba tare da sun bayar da alkaluma na adadin wadanda suka mutu ko jikkata sakamakon harin ba.

Wasu daga cikin mazauna garin sun gudu bayan sansanin sojojin ya fada hannun mayakan masu alaka da ISIS, amma wasu daga cikin  fararen hula sun fara komawa gidajensu bayan sun amince su zauna a karkashin ikon ‘yan bindigar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments