Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran sun bada labarin kama ma’aikatan Mosad na HKI a lardin Khorasan Razavi da ke arewa maso gabacin kasar, wadanda suka taimakawa HKI a kan hare-haren da ta kaiwa kasar na kwanaki 12 a cikin watan Yunin da ya gabata.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto sanarwan da dakarun suka bayar a jiya Jumma;a na cewa, bangaren leken asiri na su ya sami nasarar kama wasu mutane 8 a cikin lardin wadanda suke da hannu dumu-dumi a cikin yakin kwanaki 12 a cikin watan Yunin da ya gabata. Kuma suna aiki kai tsaye da HKI a cikin yakin.
Labarin ya kara da cewa gungun mutanen guda 8 suna aiki aikawa Mosad wurare masu muhimmanci a yankin da kuma gidaje da wuraren manya-manyan dakarin na IRGC a lardun Khurasan radawai.
Banda haka suna shirin kai hare-hare a cikin lardin tare da amfani da abubuwan fashewa da kuma wasu kayakin aikin soje wadanda aka kwace daga hannunsu. Daga karshen labarin ya kammala da cewa, an tabbatar da cewa kungiyar tana aiki kud da kud da kungiyoyi masum adawa da JMI da suke kasashen yamma. Dakarun na IRGC dai sun yabawa bangaren leken asirin nasu kan wannan kokarin nasu, na tabbatar da zaman lafiya da kuma kare kasar daga makiya daga kasashen waje.