Turkiyya Ta Bukaci A Dakatar Da Isra’ila (HKI) Daga Majalisar dinklin duniya

Majalisar dokokin kasar Turkiyya ta yi tir da kissan kiyashin da HKI take aikatawa a Gaza sannan ta amince da hana jiragen fisinja na HKI

Majalisar dokokin kasar Turkiyya ta yi tir da kissan kiyashin da HKI take aikatawa a Gaza sannan ta amince da hana jiragen fisinja na HKI wucewa ta sararin samaniyar kasar. Banda haka ta bukaci a kore daga Majalisar dinkin duniya.

Majalisar ta bukaci a kula da hakkin Falasdinawa a fagen kasashen a kuma kawo karshen yakin da ke faruwa a gaza, a ranar jumma’a ce majalisar dojojin kasar ta Turkiyya ta amince da wadannan matakan, wadanda suka dakatar da harkokin kasuwanci kwata-kwata da HKI da hana sararin samaniyar kasar ga jiragen HKI. Ya bukaci dukkan shugabannin bangariri na majalisar su sanyawa dokar hannu don ya samu matsayin gwamnatin da mutanen turkiyya gaba daya.

Kudurin ya bukaci a kafa kasar Falasdinu a kan iyakoki na shekara ta 1967. Sannan ya bayyana ncewa HKI tana da laifin hana abinci shiga gaza har saida yunwa ta kashe dubban Falasdinawa.

A wani labarin kuma kungiyar Hamas ta yi maraba da matakan da majalisar dokokin kasar Turkiyya ta dauka a kan HKI.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments