Amurka ta hana izinin shiga kasarta ga shugaban Falastinawa don halartar taron MDD

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar a jiya Juma’a cewa, sakataren harkokin wajen kasar Marco Rubio ya yanke shawarar  soke takardar izinin shiga kasar ga

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar a jiya Juma’a cewa, sakataren harkokin wajen kasar Marco Rubio ya yanke shawarar  soke takardar izinin shiga kasar ga wasu mambobin kungiyar ‘yantar da ‘yancin Falasdinu (PLO) da hukumar Falasdinu (PA), ciki har da shugaban PA Mahmoud Abbas, gabanin taron shekara-shekara na Majalisar Dinkin Duniya da za a yi a birnin New York na watan Satumba mai zuwa.

Wadannan matakai na nufin cewa da alama Abbas ba zai iya zuwa New York  don gabatar da jawabinsa na shekara kamar yadda ya saba yi ba.

Wannan mataki dai na cikin jerin takunkuman da Amurka ta kakabawa jami’an Falasdinawa a watan Yulin da ya gabata, a daidai lokacin da wasu kasashen yammacin duniya ke neman amincewa da kasar Falasdinu a hukumance.

A cewar sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar, wadannan takunkumin ba su hada da aikin hukumar Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya ba, kuma ma’aikatar ba ta bayar da wani karin bayan ikan hakan ba.

Sai dai fadar shugaban kasar Falasdinu ta bayyana matukar  mamakinta game da matakin na Amurka, inda ta jaddada cewa ya sabawa dokokin kasa da kasa da kuma yarjejeniyar MDD, musamman ganin cewa Falasdinu mamaba ce mai sa ido a MDD.

Ta yi kira ga gwamnatin Amurka da ta sake nazari tare da janye shawarar da ta yanke, tare da tabbatar da kudurinta na bin dokokin kasa da kasa.

Ma’aikatar harkokin wajen Falasdinu ta bayyana hakan a matsayin yin fatali da kudurorin MDD da aka rattaba a hannu a kansu a cikin  yarjejeniyar 1947.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments