Guinea: An Fara Tattaunawa Kan Zaben Raba Gardama Na Sabon Kundin Tsarin Mulki

A wannan makon ne aka bude damar tattauna na kowa da kowa a kasar Guinea dangane da zaben raba gardama na sabon kundin tsarin mulkin

A wannan makon ne aka bude damar tattauna na kowa da kowa a kasar Guinea dangane da zaben raba gardama na sabon kundin tsarin mulkin kasar.

Shafin yanar gizo na labarai Africa News ya bayyana cewa gwamnatin rikon kwarya na kasar ya bayyana cewa tattaunawa kan sabon kundin tsarin mulkin kasar zai gudana ne a tarurruka da kuma kafafen yana labarai na gwamnati.

Wannan dai ya sami suka daga yan jarida wadanda suke ganin kundin tsarin mulkin kasar na kowa da kowa don haka hana kafafen yada labarai masu zaman kansu gudanar da tattaunawar bai dace ba. Hakama hana jamiyyun adawa, wadanda basa dasawa da gwamnati shima bai kamata ba.

Sékou Jamal Pendessa na kungiyar yan jaridu a kasar ya bayyana cewa ba yadda zaiyu kace kana son kare hakkin fadin al-barkacin baki sannan ka hana dan adawa magana, ko kuma ka hana wani bangare na mutanen kasar magana.

Tattaunawar zai fara ne daga gobe Lahadi 31 ga watan Augusta na shekara ta 2025 zuwa ranar 18 ga watan Satumba, sannan za’a gudanar da zaben raba gardaman a ranar 21 ga watan Satumba.

Sabbin sauye sauyen da aka gabatar a wannan sabon kundin tsarin mulkin kasar dai sun hada da cewa, shugaban kasa zai yi shekaru 7  7 har sauu biyi a rayuwarsa. Za’a samar da majalisar dattawa wacce shugaban kasa zai zabi kasha 1/3 daga cikinsu.

Sojojin a kasar Ghuinea sun kwace mulki daga hannun Alpha Conde a shekara ta 2021. Daga lokacin ne batun democradiyyar kasar ya shiga matsaloli.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments