Jakadan kasar Iran a majalisar dinkin duniya Amir Saeed Iravani yayi watsi da shirin kasashen turai 3 na sake farfado da takunkuman MDD kan Iran..
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Iravani yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa Iran tana kan bakanta na tattauna da wadan nan kasashen Turai, wato Burtaniya, farana da kuma Jamus. Amma ba zata shiga tattaunawa da su tare da takura mata ba.
Iravani ya bayyana cewa kasashen turai ne suka fara sabawa yarjeniyar JCPOA, inda suka ki aiwatar da alkawulan da suka dauka a cikinta.
A halin yanzun dai kasashen turan sun bawa Jumhuriyar Musulunci ta Iran dama har zuwa wani lokaci don cika wasu sharudda kafin takunkuman su fara aiki.
Sannan daga karshe Iravani yace Iran tana goyon bayan shawarar da kasashen Rasha da China suka gabatar na samun dai-daito a cikin wannan matsalar.