Kasar Denmark Tana Goyon Bayan Dakatar Da Yarjejeniyar Kasuwacin Da Isra’ila

Gwamnatin kasar Denmark ta sanar da cewa: Tana goyon bayan dakatar da yarjejeniyar kasuwanci da haramtacciyar kasar Isra’ila Ministan harkokin wajen Denmark Lars Løkke Rasmussen

Gwamnatin kasar Denmark ta sanar da cewa: Tana goyon bayan dakatar da yarjejeniyar kasuwanci da haramtacciyar kasar Isra’ila

Ministan harkokin wajen Denmark Lars Løkke Rasmussen ya fada a ranar Asabar cewa: Kasarsa tana goyon bayan dakatar da yarjejeniyar kasuwanci da haramtacciyar kasar Isra’ila da nufin kawo karshen yakin Gaza.

Ya kara da cewa: Abin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a Gaza ya wuce kare kai, don haka dole ne a matsa lamba kanta don kawo karshen yakin da kuma bala’in jin kai.

Ya ci gaba da cewa gwamnatin mamayar Isra’ila na ruguza tsarin samar da kasashe biyu.

A nata bangaren, jami’ar kula da harkokin wajen kungiyar tarayyar turai, Kaja Kallas ta bayyana cewa: Kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun dauki mataki kan gwamnatin mamayar Isra’ila.

Ta kara da cewa, akwai rashin jituwa tsakanin kasashe mambobin kungiyar kan yadda za su tunkari gwamnatin mamayar Isra’ila, amma za a ci gaba da tattaunawa kan zabin da ya fi dacewa.

Kallas ta ci gaba da cewa, ba zai yiwu a samar da hanyoyin soji a Gaza ba, kuma matakin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi na ayyana birnin Gaza a matsayin yankin yaki ya sa al’amuran jin kai suka yi muni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted