E3 sun gindaya sharudda 3 kan dakatar da dawo da  takunkuman MDD a kan Iran

A ranar Juma’a ne Birtaniya da Faransa da Jamus suka gindaya wasu sharudda guda uku ga Iran game da batun dage mayar da takunkumin Majalisar

A ranar Juma’a ne Birtaniya da Faransa da Jamus suka gindaya wasu sharudda guda uku ga Iran game da batun dage mayar da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya a kanta,a  cikin wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar gabanin wani taron sirri na kwamitin sulhu na MDD.

Kasashen uku da aka fi sani da E3  sun ce a shirye suke su dage mayar da takunkumin har na tsawon watanni shida idan Tehran ta amince da sake baiwa masu binciken nukiliya na Majalisar Dinkin Duniya damar shiga cibiyoyinta na nukiliya, tare da  magance abin da suka kira damuwar da suke da ita game da yawan tataccen sinadarin uranium da ta ke da shi, da kuma shiga tattaunawa da Amurka.

Sabanin haka, jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saeed Iravani, ya yi watsi da tayin na Turai, yana mai bayyana shi a matsayin “mai cike da sharuddan da ba su da ma’ana,” ya kara da cewa “wadannan bukatu kamata ya yi su zama sakamakon shawarwari, ba sharuddan fara shawarwari ba.”

Iravani ya yi nuni da cewa, abin da ake bukata a halin yanzu shi ne goyon baya ga “wani takaitaccen bayani ba tare da wani sharadi ba na tsawaita kudiri mai lamba 2231,” wanda ya kafa harsashin yarjejeniyar nukiliyar ta shekarar 2015, wadda ta tanadi dage takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya da kasashen yamma suka kakabawa Iran.

A daya bangaren kuma, Rasha da China sun gabatar da daftarin kudiri ga kwamitin sulhun, inda suka bukaci da a tsawaita wa’adin kudirin har na tsawon watanni shida, inda suka bukaci dukkanin bangarorin da su koma tattaunawa cikin gaggawa. Sai dai har yanzu kasashen biyu ba su nemi a kada kuri’a a kai ba.

Jakadan na Iran ya bayyana daftarin kudurin na Rasha da China a matsayin wani mataki mai amfani na baiwa diflomasiyya karin lokaci, yana mai cewa zartar da kudurin na bukatar a kalla kuri’u tara, muddin babu daya daga cikin kasashe biyar din din din din din (Birtaniya, Faransa, Amurka, China, da Rasha) da ya yi amfani da hakkin hawa kujerar naki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments