Rwanda ta dauki bakin haure kashi na farko da aka kora daga Amurka

Cibiyar Bloomberg ta bayar da rahoton cewa, Rwanda ta karbi  rukunin farko na bakin haure da aka kora daga Amurka, a karkashin wata yarjejeniya mai

Cibiyar Bloomberg ta bayar da rahoton cewa, Rwanda ta karbi  rukunin farko na bakin haure da aka kora daga Amurka, a karkashin wata yarjejeniya mai cike da takaddama tsakanin gwamnatin kasar da  gwamnatin Donald Trump.

Mai magana da yawun gwamnatin Rwanda  Yolande Makolo ya tabbatar da cewa “rukunin farko na bakin haure bakwai da aka tantance sun isa Rwanda a tsakiyar watan Agusta.” A karkashin yarjejeniyar, Kigali ta yi alkawarin daukar mutane kusan 250, wadanda suka yi alkawarin kula da lafiyarsu, da wurin kwana, da koyar da su sana’o’i.

Canja wurin ya zama wani ɓangare na babban ƙoƙarin Washington na tura bakin haure zuwa wasu kasashe da ta kulla yarjejeniya tare da su kan hakan.

Tun daga lokacin da ya koma fadar White House a watan Janairu, Trump ya fadada irin wadannan tsare-tsare, inda ya kulla wadannan yarjejeniyoyin tare da kasashen  Rwanda,  Sudan ta Kudu da Eswatini.

Jami’an Amurka sun ce matakan sun zama dole don kawar da masu aikata laifuka masu hatsari, yayin da kungiyoyin kare hakkin jama’a ke nuna adawa da hakan.

Makolo ya kara da cewa daga cikin mutane bakwai da suka Rwanda daga Amurka, uku daga cikin sun nuna sha’awarsu ta komawa kasashensu, yayin da hudu ke fatan ci gaba da zama a Rwanda.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted