Shugaban kasar Amurka Donal Trump yayi barazanar karwa kasar China kasha 50% na kudaden fiton da zata karba daga kayakin kasar China da zasu shiga kasar, idan har bata janye maida martanin da tayi na kasha 34% dai dai karin kudin fito da Amurka ta kara mat aba.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a shafinsa na yanar gizo wato ‘Trump Social”.
Kafin haka dai shugaban kasar Amurka ya karawa kasashen duniya da dama wadanda suke huldar kasuwanci da ita kudaden fito na kayakin da suke shigo da su Amurka daga cikin har da kasar China inda Trump ya kara mata kasha 34% na dukkan kayakin China da suke shiga Amurka. Amma kwana guda bayan haka kasar China ta maida martani da kasha 34% na dukkan kayakin Amurka da suke shiga kasar China.
Amma Trump ya bawa kasar China zuwa jiya litinin 8 ga watan Afrilu da muke cikin, na ta janye karin da ta yi wa kayakin Amurka masu shiga China ko kuma ya kara wa kasar ta China kasha 50% kari kan nafarko kan kayakin kasar China masu shigowa Amurka.
Banda yake Trump yace zai dakatar da duk wata tattaunawa da kasar China kan wannan batun. Amma zata bude tattaunawa da sauran kasashen da basu maida martani ba.