Faransa, Masar da Jordan sun bukaci tsagaita wuta a Gaza

Shugabannin kasashen Faransa da Masar da kuma Jordan sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa inda suka bukaci a tsagaita bude wuta cikin gaggawa

Shugabannin kasashen Faransa da Masar da kuma Jordan sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa inda suka bukaci a tsagaita bude wuta cikin gaggawa a Gaza, tare da sukar Isra’ila kan gazawarta wajen tabbatar da ayyukan jin kai a zirin.

Kiran tsagaita wuta ya nuna bukatar samar da agajin jin kai cikin gaggawa a Gaza kuma ya nuna damuwar da kasashen duniya ke ci gaba da yi kan tashe-tashen hankula da rikicin jin kai a Gaza.

Haka kuma sanarwar wadannan kasashe uku ta nuna muhimmancin hanyar diflomasiyya na samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

A baya dai shugaba Macron ya nuna adawarsa da mamaye yankunan Falasdinawa da Isra’ila ta yi.

Macron ya kuma kira sabbin hare-haren da Isra’ila ta kai a yankin bayan rugujewar yarjejeniyar tsagaita bude wuta a tsakiyar watan Maris da cewa wani babban koma baya ne.

Sarki Abdallah na biyu na Jordan, shugaban Faransa Emmanuel Macron, da shugaban Masar Abdel Fattah el-Sisi na Masar sun bayyana cewa, “Dole ne a dakatar da yakin Gaza duba da bala’in  da ya haifar a yanzu.

Tashin hankali, ta’addanci, da yaki ba za su iya samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya ba.

Sanarwar ta yi nuni da bukatar gaggawa na kara kai kayan agaji a Gaza, inda tuni aka fara samun matsalar yunwa, da kare hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da ma’aikatan jin kai da ke aiki a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments