Jamhuriyar musulinci ta Iran, ta bayyana cewa za ta fata tattaunawa wacce ba ta kai tsaye ba da Amurka a ranar Asabar mai zuwa a kasar Oman.
Ministan harkokin wajen Iran din ne Abbas Araghchi ya bayyana hakan a shafinsa na ‘’X’’ a safiyar Talata.
“Iran da Amurka za su gana a Oman ranar Asabar don tattaunawa mai zurfi, inji ” Araghchi.
“Wannan wata dama ce, kuma kwallo yana hannun Amurka,” ta nuna da gaske ta ke in ji shi.
Kalaman Araghchi na zuwa ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa Amurka da Iran suna tattaunawa kai tsaye, bayan ganawa da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a Washington.
Shugaban na Amurka ya ce tattaunawar da za a yi tsakanin Washington da Tehran za ta kasance a matsayi mai girma.
A cikin Ofishin Oval na Fadar White House, Trump ya kuma ce: “Muna da babbar ganawa a ranar Asabar (da Iran), kuma muna mu’amala da su kai tsaye… Kuma watakila za a cimma yarjejeniya, hakan zai yi kyau.” Inji shi.
Iran dai ta sha nanata cewa a shirye ta ke ta shiga tattaunawa da Amurka amma ba bisa matsin lamba ko barazana ba.
A baya bayan nan dai shugaban Amurka ya yi barazarar amfani da bama-bamai kan Iran, idan batayi amfani da damar tattaunawar ba.