Jami’an yan sanda a birnin Makka sun tsare wata Bafalasdiniya wacce ta baje Jakarta dauke da tutar kasarta Falasdinu tare da zarginta na bayyana wani abu na siyasa a lokacin aikin umran da take yi.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Mint-Press yana cewa matar ta shiga masallacin haramin Ka’aba dauke da jakanta mai tutar falasdinu. Kuma bayan sun kamata sun tsare, Bafalasdiniyar wacce har yanzun ba’a bayyana sunanta ba, ta ce masu tana ganin wasu masu aikin umra wadanda suke shigowa masallacin Ka’aba tare da tutocin kasashen su, daga cikinsu akwai yan kasashen Morocco, Turkiyya, da sauransu, don haka itama tana dauke da tutar kasarta ce Falasdinu don nuna daga inda ta fito.
Ya zuwa yanzu dai ba wanda ya san halin da take ciki. Amma ba wannan ne karon farko wanda Jami’an tsaron kasar Saudiyya suke tsare wadanda suke dauke da tutar Falasdinu a aikin hajji ko umra ba, tare da zarginsu da cewa suna hada addini da siyasa.