A wani mataki na mayar da martani da nuna fishi, kasar Aljeriya ta yi wa jakadunta a kasashen Mali, da Nijar kiranye, tare da jinkirta aikewa da jakadanta a Burkina faso, bayan da kasashen guda uku na kawacen sahel suka dau irin wannan matakin domin goyan bayan Mali, bisa takadamar dake tsakaninta da Aljeriya biyo bayan kakkabo jirginta marar matuki.
Haka zalika ma’aikatar tsaron kasar Aljeriya ta sanar da rufe sararin samaniyarta ga dukkan jiragen da ke zuwa kasar Mali”, ba tare da bayar da wani karin bayani ba, wanda ke nuni da cewa jiragen farar hula na kasuwanci da kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa su ma abin ya shafe su.
Takaddama dai ta yi zafi tsakanin Aljeriya da Mali, inda ita ma Bamako ta sanar a yammacin ranar Litinin cewa, za ta rufe sararin samaniyarta “ga dukkan jiragen saman farar hula da na soji da ke tashi ko isa Algeria.”
Amma, rufe sararin samaniyar Aljeriya bai shafi kawayen Mali wato Nijar da Burkina Faso ba, saidai Aljeriyar ta ce ba yi nadama kan yadda kasashen suka biyu suka dau irin wannan matakin ba na goyan bayan Mali ba tare da tunani ba.
A ranar Lahadi ne Kasashe uku na AES suka sanar da yin kira ga jakadun su da ke kasar Aljeriya.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Aljeriya ta fitar, ta yi watsi da “mummunan zarge-zargen” da kasar Mali ta yi, inda ta ce Algiers ta harbo daya daga cikin jiragenta marasa matuka a kan kasarta.