Saudiyya ta bayar da wa’adin ficewar dukkanin masu aikin Umrah daga kasar

Gwamnatin Saudiyya ta ayyana 1 ga watan Dhul Qada, wadda za ta yi daidai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar karshe da duk

Gwamnatin Saudiyya ta ayyana 1 ga watan Dhul Qada, wadda za ta yi daidai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar karshe da duk wani bako da ke kasar da zummar aikin Umarah da ya fice daga ƙasar.

Sanarwar da ma’aikatar aikin Hajji da Umarah ta Saudiyya ta fitar ta ce ta dauki matakin ne domin fara gudanar da shirye-shiryen aikin Hajji mai zuwa.

Cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta ce ranar 15 ga watan Shawwal, da ya yi daidai da 13 ga watan Afrilu, ita ce ranar karshe da masu shiga kasar domin aikin Umrah za su daina shiga, sai dai a fita.

Ma’aikatar ta jaddada cewa duk wanda aka samu ya ci gaba da zama a kasar har ya wuce lokacin da kebe, to ko shakka babu ya saba ka’ida sannan kuma zai fuskanci hukunci.

Mahukuntan sun bukaci mutane da ma kamfanonin da ke shirya zuwa aikin Umrah da su kiyaye da waɗannan lokuta.

An kuma yi gargadin cewa duk wani jinkiri na barin mutane kasar za a dauke shi kamar karya doka.

Ta ce duk kamfanin da aka samu da ƙin bayyana mutanen da suka ki koma wa kasashensu to za a ci tararsu riyal dubu 100.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments