Sojojin HKI sun kara yawan hare-haren da suke kaiwa kan Falasdinawa a Gaza, a dai-dai lokacinda ake kiranta zuwa tsagaita wuta a gazar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar kungiyar kare fararen hula ta falasdinawa a Gaza, tana fadar haka a safiyar yau Talata. Ta kuma kara da cewa, Ta kuma kara da cewa a daren jiya kadai jiragen yakin yahudawan sun kashe akalla falasdinawa 19 mafi yawansu yara kanana.
Labarin ya nakalto kakakin kungiyar kare fararen hula na Gaza Mhmood Bassal yana fadar haka, ya kuma kara da crawa , a garin Deir Balah jiragen yakin yahudawan sun kai hari a kan wani gida inda suka kashe yara 5 da manyan mutane 4.
Sannan sun sake kai hare-hare kafin safiyar yau Talata a garin Beit Lahiya da kuma birnin Gaza, inda a nan ma suka kashe mutabe 10.
A jiya litinin ma sojojin HKI sun kashe fiye da mutane 24 a cikin zirin gaza gaba daya. Daya daga cikin hare-haren na jiya Litinin ya kai ga shahadar wani dan jaridar na tashar talabijin ta ‘Palastine Today’ wanda yake cikin tentin da yan jaridu suka kada a cikin asbitin Naser a garin Khan Yunus na kudancin Gaza.
Hilmi Alfaqwi ya kone kurmus a wannan harin tare da wani mutum mai suna Yusuf Al-Khazandar.