Shugaban Kasar Iran Yayi Kira Ga Kasashen Duniya Su Taimakawa Mutanen Gaza

Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya yi kira ga kasashen duniya su taimakawa mutanen gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto shugaban yana Fadar haka a taron ranar  kungiyar agaji ta ‘hillar Ahmar’ ko red cross’ ta duniya a nan Tehran. Ya kuma kara da […]

HKI Ta Bada Umurnin Rufe Ofishin Tashar Talabijin Ta Al-Jazeera A Kasar

Majalisar ministocin HKI ta bada umurnin a rufe ofishin tashar talabijin ta Aljazeera da ke birnin Nasirah a cikin kasar Falasdinu da aka mamaye. Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya bayyana cewa ministan sadawar na haramtacciyar kasar ne ya bada wannan sanarwan.  Ya kuma kara da cewa za’a rusa dakin shirye shiye na […]

Yemen: Sayyid Huthi Ya Ce Amurka Tana Yaudarar Mutane A Yakin Da Ke Faruwa A Gaza

Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen sayyid Abdullamalik Badruddeen Huthi ya bayyana cewa shugaban kasar Amurka Joe Biden yana son yaudarar mutanen ne kawai, a lokacinda ya fito ya bayyana cewa kasar Amurka zata dakatar da bawa HKI makamai ko kuma bad a yardarta ba sojojin HKI suka fara yaki a Rafah. Majiyar kamfanin dillancin […]

Shugaban Aljeriya Ya Koka Kan Ta’addancin Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Shugaban kasar Aljeriya ya bayyana cewa: An rusa duk wasu ayyukan bada agajin bil’Adama a Falasdinu Shugaban kasar Aljeriya Abdul-Hamid Taboune ya bukaci dukkanin kungiyoyin kasa da kasa da cibiyoyin bada agajin bil’Adama da su yi aiki da hakkin da ya rataya a wuyarsu wajen ganin an kawo karshen kisan kiyashin da ake yi wa […]

Tawagar Lauyoyi A Kasar Holand Sun Bukaci Gurfanar Da H.K.Isra’ila A Kotun Duniya

Wata tawagar lauyoyi a kasar Holand ta bukaci fitar da takardar sammacin neman kama Benjamin Netanyahu kan zargin aikata laifin yaki Gidan talabijin na Aljazeera ya watsa labarin cewa: Wata tawagar lauyoyin kasar Holand ta mika takardar bukatar neman kotun kasa da kasa ta ICC da  ta fitar da sammacin neman kama fira ministan gwamnatin […]

Kungiyar Hizbullahi Ta Lebanon Ta Kai Hari Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Kungiyar Hizbullahi ta Lebanon ta halaka sojojin yahudawan sahayoniyya a matsugunin yahudawa da ke arewacin haramtacciyar kasar Isra’ila A hare-haren da ‘yan gwagwarmayar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon suka kai kan matsugunin yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida da ke arewacin haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi nasarar halaka sojojin yahudawan sahayoniyya bangaren sojin Golan tare da […]

Ci Gaba Da Murkushe Daliban Jami’a A Kasar Amurka Masu Goyon Bayan Al’ummar Falasdinu

‘Yan sandan Amurka suna ci gaba da murkushe daliban jami’a da suke gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu Tashar talabijin ta NBC News ta Amurka ta watsa rahoton cewa: Rundunar ‘yan sandan Amurka sun farma daliban jami’ar Geoge Washinton da suka fito zanga-zangar nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu, inda ‘yan sandan […]

Amurka Ta Yi Furuci Da Hannu A Kashe Falasdinawa

Shugaban kasar Amurka ya yi furuci da cewa; An yi amfani da makamansu wajen kashe fararen hula a Gaza Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya amince da cewa: Tabbas an yi amfani da makaman da Amurka ta aike wa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila wajen aiwatar da kashe-kashen gilla kan fararen hulan Falasdinawa. Shugaban na Amurka […]