Shugaban kasar Amurka ya yi furuci da cewa; An yi amfani da makamansu wajen kashe fararen hula a Gaza
Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya amince da cewa: Tabbas an yi amfani da makaman da Amurka ta aike wa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila wajen aiwatar da kashe-kashen gilla kan fararen hulan Falasdinawa.
Shugaban na Amurka ya kara da cewa: Idan sojojin gwamnatin mamayar yahudawan sahayoniyya suka kai hari kan birnin Rafah yankin da ke da yawan fararen hula, ba za su samu goyon bayan Amurka ba, kuma ba za a tallafa musu da makamai ba, yana mai riya cewa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ba zata ketara jan layin Amurka kan batun kai hari kan birnin Rafah ba.