Wata tawagar lauyoyi a kasar Holand ta bukaci fitar da takardar sammacin neman kama Benjamin Netanyahu kan zargin aikata laifin yaki
Gidan talabijin na Aljazeera ya watsa labarin cewa: Wata tawagar lauyoyin kasar Holand ta mika takardar bukatar neman kotun kasa da kasa ta ICC da ta fitar da sammacin neman kama fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu da wasu jami’an gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan zargin tafka laifukan yaki a yankin Zirin Gaza na Falasdinu.
Jaridar haramtaciyar kasar Isra’ila ta Yade’ut Ahronot ta watsa rahoton cewa: Akwai yiwuwar kotun kasa da kasa mai shari’ar manyan laifuka a duniya ta ICC ta fitar da sammacin neman kama jami’an haramtacciyar kasar Isra’ila a boye, sannan bayan fitarsu daga haramtacciyar kasar ta Isra’ila a sanar da su.