Kungiyar Hizbullahi ta Lebanon ta halaka sojojin yahudawan sahayoniyya a matsugunin yahudawa da ke arewacin haramtacciyar kasar Isra’ila
A hare-haren da ‘yan gwagwarmayar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon suka kai kan matsugunin yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida da ke arewacin haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi nasarar halaka sojojin yahudawan sahayoniyya bangaren sojin Golan tare da jikkata wasu na daban.
Kafar watsa labaran gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi furuci da cewa: A luguden wutar da mayakan kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon suka yi kan matsugunan yahudawan sahayoniyya da ke arewacin haramtacciyar kasar ta Isra’ila sun halaka sojojinta tare da jikkata wasu na daban.